Yayin taron da aka yi a wannan rana, shugaba Zuma ya yi jawabi cewa, ya tsai da kudurin janye sojojin kasarsa daga babban birnin kasar Afirka ta Tsakiya, Bangui, sa'annan ya bayyana cewa, kasar na iya sake tura sojojinta zuwa kasar Afirka ta Tsakiya in akwai bukatar hakan a nan gaba.
An kira wannan taro ne don tattaunawa kan batun Afirka ta Tsakiya, inda shugabanni da dama na mambobin kasashen gamayyar tattalin arziki sun halarci taron.
Bisa labarin da aka samu, ran 23 ga watan Maris, sojoji guda 13 na kasar Afirka ta kudu sun rasu yayin musayar wuta da dakarun 'yan tawayen Afirka ta Tsakiya na kungiyar Seleka, kuma wasu sojoji guda 27 sun jikkata, kana soja guda daya ya bace.
Wannan ita ce asara mafi tsanani cikin rikice-rikicen da kasar Afirka ta Kudu ta samu tun shekarar 1994, inda hakan ya sa, bangarorin daban daban a kasar suka yi suka mai tsanani kan kudurin da shugaba Zuma ya tsayar na aikawa da sojojin kasar zuwa Afirka ta Tsakiya.
Bayan shugaba Zuma ya tsai da kudurin janye sojojin kasar, babbar kungiyar adawa ta kasar Afirka ta Kudu ta kawancen dimokuradiyya ta yi maraba da kudurin, ta kuma nuna fatan cewa, shugaba Zuma zai yi bayyani filla-filla kan lamarin ga jama'ar kasar. (Maryam)