in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasancewar kasar Afirka ta Kudu a kungiyar BRICS zai amfani Afirka
2013-06-10 16:42:31 cri

Wani jami'in gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ya fada a ranar Lahadi cewa, kasar Afirka ta Kudu za ta yi amfani da kasancewarta na mamba a kungiyar kasashen BRICS domin ta karfafa harkokin cinikayya da zuba jari da kuma hade nahiyar ta Afirka da kasashen duniya masu karfi da saurin ci gaban tattalin arziki.

Ministan cinikayya da masana'antun kasar Afirka ta Kudu Rob Davies ne ya bayyana hakan bayan taron karawa juna sani na kasashen kungiyar BRICS da aka gudanar a Johannesburg, wato kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa a halin yanzu wadanda suka hada da Brazil, Russia, India, Sin da kuma Afirka ta Kudu.

Ministan ya shaidawa mahalarta taron na BRICS na yini guda cewa, kasar Afirka ta Kudu ta shiga kungiyar ce, domin ta yayata kasar, kana ta hade nahiyar, baya ga cewa, kasa ce mai tasowa, sannan wani bangare ne na nahiyar Afirka.

Ya ce wajibi ne Afirka ta Kudu ta rungumi tsarin inganta masana'antu, ta yadda nahiyar mai yawan al'umma sama da biliyan 1.1 za ta amfana da tattalin arzikin nahiyar da ya kai dala triliyan 2.

Ya kuma bayyana cewa, kasar Afirka ta Kudu za ta mayar da hankali wajen inganta kayayyakin more rayuwa a shirinta na gaba na bunkasa tattalin arziki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China