A bikin shirya kasancewar kungiyoyi cikin rukuna da aka yi a hedikwatar hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF), dake birnin Alkahira na Masar ranar Asabar din da ta gabata, an tabbatar da cewa, kasashen Najeriya, Morocco, Aljeriya da Senegal sune zasu yi wasanni a rukuni na biyu
Bayan yanke shawarar da CAF din ta yi na sauya salon wasannin karshe na neman cancantar shiga gasar wasannin Olympics zuwa na gasar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekaru 23, yanzu ta tabbata cewar, za'a dinga yin irin wannan gasa cikin shekaru hurhudu ana shekara guda kafin gasar Olympics din.
Daga ranar 26 ga watan Nuwamba zuwa ta 10 ga watan Disamba ne za'a gudanar da gasar ta farko.
Robin Petersen, babban jami'in hukumar kwallon kafa ta kasar Afirka ta Kudu (SAFA), daya kasance a wajen bikin shirya kungiyoyin ya ce, kalubale ne babba a gabansu,don duk kungiyoyin da zasu yi wasa a rukuninsu suma suna da karfi, kuma dukkan kungiyoyin takwas masu kafri ne. Sai dai ya bayyana cewar, kungiyar kasar Afirka ta Kudu zata yi kokarin samun sakamakon da zai kai ta ga samun gurbi a gasar wasannin Olympics din. (Garba)