Chen Xiaoxing ya bayyana wa 'yan jaridan kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, bayan da aka kammala zaben shugaban kasar Nijeriya, za a samu babban ci gaba kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Nijeriya, kana shiyar Lekki da kasashen biyu suka gina cikin hadin gwiwa, za ta samu sabon ci gaba.
A ganin Chen Xiaoxing, shiyar Lekki za ta kasance wani sabon birni dake mashigin tekun Guinea, bayan da aka samar da kayayyakin more rayuwa a shiyar, za ta kasance cibiyar musayar kayayyaki a yankin yammacin nahiyar Afirka.(Zainab)