Liu Xianfa, karamin jakadan kasar Sin da ke Lagos ya ce, yankin Lekki yana zamanto sabon karfin da zai kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin Nijeriya, haka kuma zai taka rawa wajen inganta dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Nijeriya cikin sauri.
Babatunde Fashola, shugaban jihar Lagos ya ce, yin hadin gwiwa da kasar Sin yana iya kyautata karfin Nijeriya na kawo albarka, da inganta kwarewar masana'antun Nijeriya ta yin takara a kasuwannin duniya. Wannan kuma shi ne muhimmin dalilin da ya sa yankin Lekki ya samu goyon baya daga wajen Nijeriya, wanda kuma ya samu nasara. (Tasallah)