An kira wani taron manema labaru a yankin cinikayya maras shinge na Lekki dake jihar Lagos Tarayyan Nijeriya wanda Sin da Nijeriya suka yi hadin gwiwwa wajen kafa shi a ran 7 ga wata, inda aka sanar da cewa, za a kaddamar da dandalin tattaunawa kan zuba jari da bikin baje kolin kayayyaki na jihar Lagos a ran 3 ga watan Agusta.
A gun taron, babban direktan yankin Lekki Chen Xiaoxing ya ce, dandalin a wannan karo ya fi na ko wane girma da aka yi a da can baya, wanda ke da jigon "Manufofi, hidima da zuba jari", za a mai da hankali ne kan tabbatar da manufofin da suka shafi wannan yanki, kafa tsarin ba da hidima, zabo wani tsarin raya yanki mai kyau da yadda za a bunkasa Nijeriya nan gaba da sauransu.
Chen ya ce, shugabanni da dama za su halarci taron, ciki har da ministan kula da harkar zuba jari da ciniki na Nijeriya, jakadan kasar Sin dake Nijeriya da wakilan 'yan kasuwa da sauransu inda za su tattauna kan hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen biyu.
A sa'i daya kuma, wakilan kamfanoni fiye da dari za su yi musayar ra'ayoyi domin neman yin hadin kai da kawo moriyar juna. Dadin dadawa, a gun bikin baje kolin kayayyaki na jihar Lagos, za a gabatar da dubban kayayyaki ciki har da motoci, abinci, kayayyakin sake-sake, injuna da sauransu.(Amina)