Yau Jumma'a 25 ga wata ne, aka yi taron manema labarai da kamfanin hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen zuba jari a yankin Lekkin na kasar Najeriya ya kira, inda shugabannin kamfanin, gami da 'yan jaridu daga kafofin watsa labarai da dama na kasar Sin suka halarta.
A halin yanzu, gwamnatin kasar Sin na kokarin aiwatar da manufar baiwa kamfanoninta kwarin-gwiwar su fita domin su habaka harkoki a kasashen ketare, musamman ma a karfafa hadin-gwiwa da mu'amala ta fuskar cinikayya tare da kasashen Afirka. Yankin ciniki maras shinge na Lekki, wanda aka fi sani da suna Lekki Free Trade Zone na daya daga cikin ababen misali na hadin-gwiwar kasashen Sin da Najeriya.
A wajen taron da aka yi Jumma'ar nan, shugabannin kamfanin hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen zuba jari a yankin Lekki sun yi jawabi, inda mai kula da kamfanin, Mista Zheng Jun, a cikin jawabinsa na maraba, yayi bayanin cewa, ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, kamfanin ya zuba kudi dala miliyan 88 ga yankin, kuma gwamnatin kasar Sin ta bada tallafin Yuan miliyan 120 a wannan aiki. A halin yanzu, in ji shi, akwai kamfanoni 28 wadanda suke tafiyar da ayyukansu a yankin Lekki, ciki har da masana'antar kera motoci, da ta harhada magunguna, da ta samar da kayan gida, gine-gine, masu kula da sarrafa man fetur, da sauransu.
Jawabin da Mista Zheng Jun yayi ya fi jawo hankalin jama'a shi ne, ya ce, yankin Lekki ba yanki ne na hadin-gwiwar kamfanonin Sin da Najeriya kawai ba, a halin yanzu, ana kokarin raya shi har ya zama wani yankin ciniki maras shinge na kasa da kasa. Alal misali, yankin na jawo hankalin wasu manyan kamfanonin duniya su zo su zuba jari, kamar su kamfanoni daga kasashen Birtaniya, Afirka ta Kudu, Italiya, Indiya da sauransu.
Shi ma a nasa bangaren, jami'in kula da harkokin jawo jari na kamfanin, Mista Wei Xuemin ya bayyana muhimmancin kasar Najeriya ga kasar Sin a fannin zuba jari, inda ya ce, birnin Ikko, cibiyar tattalin arziki da ta cinikayya ce a Najeriya har ma a yankunan yammacin Afirka baki daya, kuma kayayyakin kasar Sin na samun karbuwa sosai a wannan wuri. Mista Wei ya yabawa gwamnatin Najeriya saboda rangwame da saukin da take kawowa kamfanin wajen raya yankin ciniki maras shinge na Lekki, yana fatan gwamnatocin kasashen biyu za su kara hadin-kai wajen bullo da wata yarjejeniya domin taimakawa ci gaban wannan yanki, musamman ma a karkashin tsarin dandalin tattaunawa na hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka.(Murtala)