in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara tattaunawa kan yankin cinikayya cikin 'yanci mafi girma a nahiyar Afrika
2011-06-13 10:46:15 cri

Ranar Lahadi 12 ga wata a birnin Johannesburg hedkwatar tattalin arzikin kasar Afrika ta kudu, shugabanni da wakilan gwamnatin wasu mambobi kasashe na kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afrika, kungiyar bai daya ta gabashin Afrika (EAC) da kungiyar raya kudancin Afrika baki daya sun yi taron koli a karo na biyu na bangarorin uku, kuma sun sanar da fara yin shawarwari kan yankin cinikayya cikin 'yancin mafi girma a nahiyar Afrika.

Wannan taron koli mai taken "sa kaimi ga raya bangarorin uku bai daya", da zummar kafa wata kasuwa bai daya. Taron ya bayyana cewa, a cikin shekaru 3 masu zuwa, za a yi kokarin tabbatar da cinikayyar kayayyaki cikin 'yanci tsakaninsu, da samar da tushe mai inganci wajen bunkasa cinikayyar ba da hidimma da zuba jari cikin 'yanci.

Kafin wannan kuma, kungiyar bai daya ta gabashin Afrika, kungiyar raya kudancin Afrika baki daya da kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afrika sun fara kafa yankin cinikayya cikin 'yanci a shekarar 2005, 2008 da 2009 domin samar da zarafi mai kyau wajen kafa yankin cinikayya cikin 'yanci bai daya. Ko da yake akwai gibin tattalin arziki tsakaninsu, kuma ana karancin bunkasa manyan ayyukan more rayuwa da rashin kwadagon aiki da dai sauran waharhalu.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China