in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin injuna karo na biyu a yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki
2011-11-23 10:37:09 cri
Ranar Talata 22 ga wata, an bude bikin baje koli na injuna karo na biyu a yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki dake Lagos cibiyar kasuwancin kasar Nijeriya. Sin da kasar Nijeriya sun hada kai domin kafa wannan yanki.

A gun bikin budewa, shugaban kamfanin raya yankin Lekki Chen Xiaoxing ya ce, shekarun nan baya, yankin ya samu ci gaba mai armashi, al'amarin da ya kara samar da hadin kai tsakanin kasashen Sin da Nijeriya. Wannan bikin baje koli da aka yi a yankin ya samar da wani dandali mai kyau ga kasashen biyu harma ga kasashe daban-daban wajen yin musayar ra'ayi da yin hadin kai a fannin injuna da na'urori. Za a mai da wannan yanki a matsayin wani sabon birni da zai bunkasa zuwa wata cibiyar cinikayya a kasar Nijeriya har ma a dukkan nahiyar Afrika.

Karamin jakadan kasar Sin dake birnin Lagos mai kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya Jia Ping shi ne ya kaddamar da wannan bikin. Yana fatan wannan yanki zai sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar hadin kai tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

An ba da labari cewa, an kafa wannan yanki a tsibirin Lekki dake da nisan kilomita 50 daga cibiyar birnin Lagos yawan fadinsa da aka tsara ya kai muraba'in kilomita 165.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China