Bisa labarin da aka samu, an ce, an gudanar da wannan aiki ne na bada taimakon jinya bisa hadin gwiwar gwamnatin kasar Sin, da kungiyar kasuwancin kamfanonin Sin da ke kasar ta Zimbabwe.
A dai wannan rana, masana 10 na tawagar aikin jiyya ta Sin, na tawaga ta 13 ne suka gudanar da aikin duba lafiyar jama'a. Halin kiwon lafiyar yankin dai na da karanci, don haka matakin ya sa mazauna wurin masu fama da taulauci, ke matukar nuna godiya ga taimakon da likitocin suke ba su.
Shugaban tawagar ma'aikatan jinyar Deng Lipu, ya bayyana cewa, tun lokacin da kasar Sin ta fara tura tawagar ma'aikatan jinya zuwa kasar Zimbabwe a karo na farko cikin shekarar 1980, ya zuwa yanzu, tawagogi sama da 13, da suka kunshi likitoci fiye da 140 ne suka gudanar da aiki kasar.
Bugu da kari, a cewar mista Deng, shekarar bana ita ce cikon shekaru 50 na wannan aiki na tura lokitoci zuwa kasashen Afirka da gwamnatin kasar Sin ke gudanar, tawagar ba da jinya ta Sin zata ci gaba da dukufa kan wannan aiki, don karfafa zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma ba da taimako ga jama'ar kasar Zimbabwe. (Maryam)