Mr. Makadji ya nuna yabo sosai ga ayyuka da kuma halayen ma'aikatan rukunin ba da jinya na kasar Sin, inda ya yi godiya gare su domin gudumawar da suka bayar kan inganta harkokin hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya da kuma zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu.
Bisa labarin da aka samu, ana da ma'aikata sama da 30 cikin rukunin, wadanda suka isa kasar Mali a watan Agusta na shekarar 2011, kuma yayin da suke gudanar da ayyukansu a kasar Mali, sun ba da gudumawa sosai a fannin kiwon lafiya na kasar. (Maryam)