in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana cikin halin tsaka mai wuya a Siriya
2013-08-30 16:49:38 cri

Kwanan baya, kasashen yammacin duniya sun kara jaddada cewa, za su dauki matakin soji kan kasar Siriya, sakamakon haka, mai yiwuwa ne, za a dauki matakan soji kan kasar Siriya don warware rikicin kasar. A sa'i daya kuma, kasashen da suke adawa da yaki, su ma suna ta tattaunawa, don kokarin warware rikicin kasar Siriya ta hanyar siyasa.

Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Amurka suka bayar a ranar 29 ga wata, an ce, jiragen ruwan yaki masu dauke da rokoki na sojojin Amurka su isa Bahar Rum da ke kusa da kasar Siriya a wannan rana da dare, wato ke nan, sojojin Amurka sun jibge jiragen ruwan yaki da yawansu ya kai 5 a wurin, kuma dukkansu na iya harba rokoki. Bisa labarin da aka bayar, an ce, shugaban kasar Amurka Barack Obama zai ba da umurni ga sojojin kasar, don amfani da jiragen ruwan yaki masu dauke da rokoki don kai farmaki ga kasar Siriya. Ban da wannan kuma, a ranar 29 ga wata, mambobi 140 na majalisar wakilan kasar sun rubuta wata wasika ga shugaban Obama, don bukatar shi da ya samu amincewa daga majalisar dokoki, kafin ya ba da umurnin daukar matakin sojin.

A ranar 29 ga wata, shugaban kasar Turkiyya Abdullah Gul da firaministan kasar Recep Tayyp Erdogan sun shirya taron koli ta fuskar tsaro, inda suka tattauna shirin daukar matakin soji kan kasar Siriya, da kuma rawar da Turkiyya za ta taka idan kasashen yammacin duniya sun amince da daukar matakan soji ga kasar Siriya.

Ban da wannan kuma, a ranar 29 ga wata, majalisar dokokin kasar Birtaniya ta shirya wani taro, don tattauna batun shigar da kasar cikin yakin, idan kasar Amurka ta dauki matakan soji ga kasar Siriya. Firaministan kasar Birtaniya David Cameroon ya amince da cewa, yanzu, babu cikakkiyar shaidar da ta nuna cewa, za a kai farmaki. Sai dai ya kamata akasarin 'yan majalisar dokoki su amince da kudurin daukar matakan sojin, yanzu, ba kawai cikin majalisar dokokin kasar ba, har ma cikin jam'iyyar da ke mulkin kasar, akwai mutane da dama da suke adawa da daukar wannan mataki. A wannan rana, David Cameroon ya bayyana cewa, kafin rukunin bincike na M.D.D. ya bayar da sakamakon bincike, Birtaniya ba za ta dauki matakan soji kan kasar Siriya ba. A wannan rana, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Birtaniya ya bayyana cewa, Birtaniya za ta tura jiragen saman yaki Typhoon zuwa sansanin Akrotiri, don daukar matakan soji wajen tabbatar da moriyar kasar Birtaniya, kuma wadannan jiragen saman yaki ba za su shiga cikin matakan soji ba.

A ranar 29 ga wata, a fadar shugaban kasar Faransa Elysée, shugaban kasar Francois Hollande ya yi shawarwari da jagoran bangaren adawa na kasar Sirya, inda ya bayyana cewa, ya kamata a yi kokarin warware batun Siriya ta hanyar siyasa, amma dole ne bangaren adawa na kasar ya samu kwarewa sosai wajen warware batun ta hanyar siyasa, musamaman ma batun kwarewa wajen harkokin soji. A sa'i daya kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su mayar da martani yadda ya kamata, don hana halin da ake ciki a kasar Siriya zai kara tsananta.

Game da kalubalan aikin da kasashen yammacin duniya suke yi shirin, a ranar 29 ga wata, shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad ya bayyana cewa, Siriya za ta yi yaki da ko wane dan mulkin mallaka, don kare kanta. Bashar ya bayyana cewa, barazanar kai farmaki ga kasar Siriya zai kara karfafa zukatan jama'ar Siriya, kuma idan aka kai mata farmaki, tabbas ne Siriya za ta mayar da martani. A wannan rana, ministan tsaro na kasar Siriya kuma mataimakin kwamanda na sojojin kasar Fahd Jassemal Freij ya bayyana cewa, sojojin kasar da jama'a za su mayar da martani game da farmakin soji da za a kai wa kasarsu.

A sa'i daya kuma, kasashen duniya suka shirya taron tattaunawa cikin gaggawa, don warware rikicin kasar Siriya ta hanyar siyasa. A ranar 29 ga wata da yamma, wakilan kasashe 5 da ke da kujeru din-din-din a kwamitin sulhu na M.D.D. sun shirya taron gaggawa karo na biyu game da halin da ake ciki a kasar Siriya, amma ba su cimma matsaya guda ba. Game da taron tattaunawa da suka yi cikin siri, daga bisani kuma, wakilan mahalartar taron sun ki bayar da sharhi ga kafofin yada labaru game da yadda taron yake, sabo da haka, ba a san yadda taron ya wakana ba.

A ranar 29 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya buga waya ga bangarorin da batun ya shafa, game da halin da ake ciki a kasar Siriya, Wang Yi ya sake jaddada cewa, game da batun yaki, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su yi hakuri. Yin shawarwari ta hanyar siyasa ya zama hanya kadai da za a bi wajen warware batun kasar ta Siriya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China