A ranar 1 ga wata, wasu jama'ar kasar Siriya sun yi zanga-zanga a wurin da ke kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Damascus na kasar Siriya, don nuna adawa ga sanarwar daukar matakan soji kan kasar da shugaban kasar Amurka Baraka Obama ya bayar a ranar da ta gabata.
Yayin da jama'ar kasar Siriya suke kara nuna adawa ga yaki, a ranar 28 ga watan Agusta, kasar Jordan da take makwabtaka da Siriya, ta ba da sanarwa don nuna matsayin da ta dauka na tsaka-tsaki. Game da sanarwar da shugaban Obama ya bayar a ranar 31 ga watan Agusta, a gun taron manema labaru da aka yi a fadar firaministan kasar, ministan yada labaru na Jordan kuma kakakin gwamnatin kasar Muhammad Momani ya bayyana cewa, Jordan ta nace kan warware batun Siriya ta hanyar siyasa, kuma ba ta nuna goyon baya game da yin shisshigin soji a kasar ba.
Fadar White House ta Amurka ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta amince da daukar matakan soji kan kasar Siriya, a ranar 1 ga wata, kungiyar hadin gwiwa kan kasashen Larabawa AL ta shirya wani taron ministocin harkokin waje cikin gaggawa, don yunkurin cimma matsaya guda game da rikicin kasar Siriya. Amma, game da sabanin ra'ayi dake tsakanin goyon bayan Amurka da ta dauki matakan soji kan Siriya, kasashen Masar, Iraqi, Lebanon, Tunisiya, da Aljeriya sun nuna adawa da matakin soji da Amurka take so ta dauka, don haka gamayyar kasashen Larabawa ta kasa cimma matsaya guda kan wannan batu.(Bako)