Von Rompuy ya ce, ya kamata a warware batun Siriya a karkashin inuwar M.D.D., kuma ba zai yiwu a warware batun ta hanyar soji ba, ya ce, hanyar da ta fi dacewa a bi ita ce, siyasa.
A wannan rana, kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya sake jaddada cewa, kwamitin sulhu na M.D.D. shi ne kawai zai iya amince da daukar matakan soji a fannin dangantakar kasa da kasa, kuma wasu kasashe da ke zargin Siriya ta yi amfani da makamai masu guba bisa ganin damarsu, ba su dauki matakin da ya dace da huruminsu ba.
A wata sabuwa kuma, a ranar 5 ga wata, kafofin yada labaru na kasar Turkiyya sun bayyana cewa, yanzu, ana ci gaba da jibge sojojin kasar a kan iyakokin da ke tsakaninta da kasar Siriya, don tinkarar kalubale daga kasar ta Siriya. Haka kuma, kwanan baya, shugaban kasar Turkiyya, da firaministan kasar sun bayyana cewa, idan aka tabbatar da gwamnatin Siriya ta yi amfani da makamai masu guba, kasar Turkiyya, za ta goyi bayan daukar matakan soji kan kasar Siriyan.(Bako)




