in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hare-hare guda biyu a kasar Pakistan
2013-07-01 17:04:13 cri
A ranar 30 ga wata, an kai hare-hare har guda biyu a kasar Pakistan, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 10. Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari da firaministan kasar Nawaz Sharif sun yi Allah-wadai da harin, tare da janjanta wa dangogin mutanen da suka rasu.

A ranar 30 ga wata, bangaren 'yan sanda na Pakistan ya sanar da cewa, an kai harin kunar bakin wake a wani masallacin da ke makarantar addini na birnin Quetta da ke kudu maso yammacin kasar, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 28, cikinsu har da mace guda da yara 3, tare da jikkatar wasu sama da 60. Majiya labarin ya bayyana cewa, wani mahari ya tayar da bom da aka daura a jikinsa a masallacin.

A wata sabuwa kuma, a tsakiyar wannan rana, an kai hari ga ayarin motoci na rundunar soji ta kasar a yankin karkara na birnin Peshawa da ke arewacin kasar Pakistan, abin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 14, tare da jikkatar wasu 25. Wani jami'in wurin ya bayyana cewa, lokacin da motoci 3 na rundunar soji suka wuce yankin karkara na birnin Pashewa, bam ya tashi a cikin wata mota, abin da ya shafi wata kasuwa da ke kusa da wurin, haka kuma, cikin mutanen da suka rasu ko raunata, har da fararen hula da dama, da kuma yara.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China