in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin da batun Siriya ya shafa da su kai zuciyar nesa
2013-08-29 10:09:43 cri

A ranar 28 ga wata, yayin da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ke zantawa da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi game da ra'ayin kasar Sin kan halin da ake ciki a kasar Siriya, minista Wang ya bayyana cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai game da halin da ake ciki a kasar Siriya. Kasar Sin tana adawa da ko wane bangare kan amfani da makamai masu guba a kasar Siriya, kuma tana goyon bayan rukunin masu bincike na M.D.D. da ya gudanar da bincike cikin adalci, a bayyane, kuma da kanta. Kada a kawo cikas game da aikin bincike na yanzu, domin baiwa wannan tawaga damar yin aikinta, kuma kada a bada sakamako bisa kimantawarsu kafin an gama binciken.

Wang Yi ya jaddada cewa, shawarwari sun kasance hanyar daya tak da za a bi wajen warware batun kasar Siriya. Yin shisshigin soji zai saba da dokokin M.D.D. da ka'idoji na dangantakar kasa da kasa, kuma zai tsananta halin da ake ciki a yankin Gabas ta tsakiya. Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa, don nacewa kan bin daidaitaciyyar hanya ta warware rikicin Siriya ta hanyar siyasa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China