A ranar Lahadin nan, shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya ce, gwamnatinsa za ta rage tallafin mai ne a matsayin wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin kasar.
Shugaban wanda ya yi bayanin haka a wani taron manema labarai a birnin Khartoum ya ce, akwai matakai da yawa da za su taimaka a yi kwaskwarima ga tattalin arzikin kasar bayan da ta yi asarar kashi biyu a cikin uku na kudin shiga da take samu daga man fetur sakamakon rabuwarta da Sudan ta Kudu.
A cikin wadannan sabbin matakai, in ji shi, akwai cire tallafin a man fetur da sauran wassu kayayyakin masarufi, yana mai lura cewa, an dauke wadannan matakai ne saboda tallafin man fetur kawai ya kai kudi kimanin dalar Amurka biliyan 1.7 a ko wace shekara.
Haka kuma ya jaddada cewar, tallafin man fetur din ya zama barazana ga tattalin arzikin kasar, abin da ke kara kawo hauhawar farashin kayayyaki da tabarbarewar kudin kasar.
Don haka, shugaba al-Bashir ya yi bayanin cewar, kwaskwarimar a kan tattalin arzikin wadda ake sa ran a fara ta nan ba da jimawa ba tana da kudirin kara kudin shiga da samar da kayayyakin bukata, da kuma rage kudaden da ake kashewa. (Fatimah)




