Akalla mutane 53 suka mutu a yayin da 77 suka jikkata a cikin haduran dake da nasaba da ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma ambaliyar ruwa da aka samu a yawancin yankunan kasar Sudan, in ji ministan cikin gidan kasar Sudan a ranar Alhamis a birnin Khartoum. A dunkule iyalai 40,578, wannan lamari ya rutsa da su tare da kuma lalata gidaje 20,027 a dukkan fadin kasar, in ji minista Ibrahim Mahmoud Hamid a yayin wani taron manema labarai. Haka kuma jami'in ya kara da cewa, ruwan sama da ambaliyar ruwa sun kashe dabbobi dubu uku, haka zalika, lamarin ya shafi ma'aikatan kadarorin gwamnatin kasar 251, kuma yawancinsu makarantu ne. (Maman Ada)