Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samo mana labarin cewa, a ranar Lahadin nan sojojin kasar Sudan suka samu nasarar kwato kauyen Ashambo dake cikin wani yanki na jihar Blue Nile, kamar yadda kakakin rundunar Al-Sawarmy Khalid Sa'ad ya sanar.
Al-Sawarmy ya ce, sojojin kasar sun samu nasarar samar da 'yanci ga mazauna kauyen Ashambo a yankin Gaisan dake jihar Blue Nile dake kan iyaka da Sudan da kasar Habasha inda a kwanakin baya wani bangaren kungiyar 'yan tawaye mallakar SPLM daga shiyyar arewa suka shiga kauyen suka kona kasuwa, sannan suka yi ma mazauna wuren sata,
Kakakin ya yi bayanin cewa, sojojin kasar sun shiga wannan kauye inda suka yaki da wadannan 'yan tawaye suka 'yantar da mazauna wurin su dai 'yan tawayen, in ji kakakin, sun tsere amman an kashe yawancinsu a cikin arangamar kuma ana bin sawun sauran da suka tsere.
Jihar Blue Nile dai ta dade tana fuskantar arangama tsakanin sojojin kasar da 'yan tawaye na kungiyar SPLM a shiyyar arewa tun shekarar ta 2011. (Fatimah)




