in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 100 suka mutu sakamakon fadan kabilanci a Darfur na Sudan
2013-08-12 10:14:35 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu mana labari daga kasar Sudan cewa, akalla mutane 100 ne suka halaka a wani sabon fadan kabilanci da ya barke tsakanin kabilu biyu na Larabawan dake yankin Darfur.

Fadan ya kaure tsakanin kabilar Rizaigat da na Ma'liya a shiyyar Adila dake kudancin Darfur inda kowannensu ke dauke da makamai a ranar Asabar, kamar yadda wani daga kabilar Rizaigat da ya shaida ma Xinhua ya ce, kabilarsa ta kashe 'yan kabilar hamayya da su Ma'liya guda 70 su kuma nasu 'yan kabilar 30 suka bace, sannan aka jima mutane 70 rauni.

Yana mai cewa, har yanzu hankali bai kwanta ba, abin da ke nuna yiwuwar sake arangama nan gaba.

Fadan kabilanci ya zama babban muhimmin batu a yankin wanda ke fuskantar gwamnatin kasar Sudan, wadda har yanzu ta gagara shawo kanshi duk da manyan taruka da take ta kira tsakanin kabilu domin sulhuntawa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China