in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattaunawa tsakanin Khartoum da Juba ta rage zaman dar dar a kan iyakokin kasashen
2013-08-30 10:06:50 cri

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun kammala tattauanawa ta fannin tsaro a tsakaninsu, abin da ya rage zaman dar dar da ake yi a kan iyakokin kasashen biyu, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Sudan SUNA ta ruwaito sanarwar kakakin. rundunar sojan Sudan, Al-Sawarmy Khalid Saad.

Shi dai tattaunawar, an yi ta ne a matsayin wani cigaban ayyuka na warware takaddamar da ake yi a kan iyakokin kasashen, in ji kakakin. An fara zaman dar dar ne a garin Joda Dabatal-Fakhar a farkon wannan makon lokacin da sojojin kasar Sudan ta Kudu kusan su 100 suka shiga garin ta bakin iyaka da ya hada kasashen biyu.

Kamar yadda Al-Sawarmy Sa'ad ya yi bayani, yanzu dai sakamakon tattaunawar da aka yi da tuntunbar juna, an yi zaman na musamman inda aka cimma matsaya da aka warware matsalar.

Ya ce, rundunar tsaro ta kasashen biyu ta samu damar shawo kan matsalar da ake tsoron zai auku ta hanyar samar da motoci da sauran ababen bukatu don gudanar da tsaro yadda ya kamata, yana mai nuni da cewa, jami'an tsaro za su ci gaba da kula da yankunan dake kan iyakokin kasashen biyu domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China