Kafar yada labaran yanar gizo ta Ashrouq da ke Sudan, ta bayyana cewa, kimanin mutane 39 ne suka mutu ranar Laraba sakamakon wasu fadace-fadacen kabilanci tsakanin kabilu biyu a yankin Darfur na kasar Sudan.
Kwamishinan yankin Abu Karinka da ke jihar gabashin Darfur, Osman Qassim, ya ce, an kwashe kusan sa'a guda ana gwabza fada da makamai tsakanin 'yan kabilar Ma'liya da Rizaigat a Bakheet da ke yankin Abu Karina, inda mutane 39 suka mutu yayin da wasu 47 suka jikkata daga bangarorin biyu.
A ranar 11 ga watan Agusta ne fada ya barke tsakanin sassan biyu, inda sama da mutane 100 suka rasa rayukansu, lamarin da ya sa gwamnatin Sudan ta shawo kan shugabannin kabilun biyu, da su sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna.
Fadan kabila, ya kasance abin da ke damun gwamnatin Khartoum, duk da tarukan sasantawa da dama da aka gudanar tsakanin kabilun da ke gaba da juna. (Ibrahim)




