in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a tattauna batun Syria bisa tsarin kwamitin sulhun MDD, in ji ministan harkokin wajen Sin
2013-09-09 10:22:33 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a ranar Lahadi da yamma a birnin Tachkent cewa, batun rikicin Syria ya kamata a tattauna shi bisa tsarin kwamitin sulhu na MDD. Mista Wang dake rakiyar shugaban kasar Sin Xi Jinping dake ziyarar aiki a kasar Ouzbekistan, ya bayyana matsayin kasar Sin kan rikicin kasar Syria a yayin wata hira ta wayar tarho tare da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry.

A yayin wannan tattaunawa, mista Wang ya jaddada cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta tsaya bisa muhimman ka'idoji biyu game da batun Syria, wato girmama dokokin tushe dake tafiya da tsarin dangantakar kasa da kasa da kuma watsi da yin amfani da makamai masu guba. Domin haka ne, ya kamata a maido da batun rikicin Syria bisa tsarin kwamitin sulhu na MDD, inda bangarorin da abun ya shafa za su iyar bullo da hanyar da ta dace wajen cimma matsaya guda, in ji mista Wang.

A matsayin kasashe masu kujerar din din din a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin da kasar Amurka ya kamata su dauki matakin kare sharudan kundin MDD da baiwa kwamitin sulhu 'yancinsa na daukar nauyinsa kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, in ji ministan harkokin wajen kasar Sin, tare da jaddada adawar kasar Sin ga duk wani matakin amfani da karfin soja a cikin harkokin kasa da kasa, kana kuma da yin kira ga kasashen da wannan lamari ya shafa da su yi tunani mai zurfi game da duk matakin soja kan kasar Syria. Haka zalika, bangarorin biyu sun dauki alkawarin cigaba da tuntubar juna kan batun Damascus. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China