in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD na kokarin bullo da wani salo na kawo karshen batun Syria
2013-09-05 10:44:32 cri

Shugaban kwamitin sulhu na MDD Gary Quinlan ya fada a ranar Laraba cewa, kwamitin majalisar zai duba bukatar da ke akwai ta kawo karshen batun zargin amfani da makamai masu guba da ake yi a Syria, ganin yadda wannan batu ya kartata ga taron kolin G20 da za a yi a birnin St. Petersburg na kasar Rasha, inda shugabannin duniya za su gana a kwanaki masu zuwa.

Shugaban ya ce, ya amince cewa, batun ba ya cikin ajandar kwamitin a hukumance, amma mambobin kwamitin sun gana a bayan fage da babban sakataren MDD Ban Ki-moon kan yadda za a tunkari batun na Syria.

Ya ce, jakadun kasashe da ke cikin kwamitin, sun damu matuka kan binciken da MDD ke gudanarwa game da zargin amfani da makamai masu guba, wato kan yadda za a gudanar da shirin yadda ya kamata, cikin hanzari, kiyaye martabar tsarin bincikin kimiyya, da kuma batun yaushe ne za a kammala da kuma bukatar ganin an jira kafin daukar duk wani irin mataki.

Ko da yake, ganin yadda ake kokarin warware wannan batu na Syria, kamata ya yi a kara kokari ta fuskar diflomasiya, tun da yanzu hankali ya koma ga taron kolin G20.

Gary Quinlan ya yi nuni da cewa, yanzu dai dukkan shugabannin kasashe masu kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD wato kasashen Burtaniya, Sin, Faransa, Rasha da kuma Amurka za su halarci taron kolin G20 da za a yi a St. Petersburg, da kuma kasashen da ba su da kujerun din-din-din a kwamitin sulhun wato Australia da Koriya ta Kudu wadanda su ma mambobin kungiyar G20 ne tare da sauran muhimman kasashe, sun bayyana karara cewa, batun Syria yana daga cikin abin da suke son tattaunawa a taron.

Ko da yake wannan batu ba ya cikin jerin ajandan taron, amma shugaban kwamitin sulhun ya gamsu cewa, za a tabo batun yayin tattaunawar kasashe ko na sauran kungiyoyi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China