Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya bar Yamai a ranar Laraba da yamma zuwa birnin Bamako na kasar Mali tare da wata babbar tawaga bisa goron gayyata na hukumomin Mali domin halarta bikin rantsar zababen shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita (IBK) da zai gudana ranar yau Alhamis. Bayan rantsuwar kama aiki a ranar 4 ga watan Satumban, za'a shirya wani babban bikin liyafa a ranar Alhamis inda shugabannin kasashe 26 za su halarci wannan biki, daga cikinsu, akwai shugaban kasar Faransa Francois Hollande.
An zabi shugaba Ibrahim Boubacar Keita a ranar 11 ga watan Agustan da ya gabata, kuma kafin ya yi rantsuwar kama aiki, sai da ya kai wata ziyara a birnin Yamai a ranar 1 ga watan Satumban domin jinjinawa kasar Nijar da al'ummarta kan taimakon da suka bayar wajen warware rikicin kasar Mali.
Kasar Nijar dai ta tura sojoji 680 a cikin tawagar tallafawa Mali ta kasa da kasa (MISMA) tun farkon barkewar rikicin kasar a cikin watan Janairun da ya gabata domin fatattakar kungiyoyin ta'adancin da suka mamaye arewacin kasar Mali, tare da kwato 'yancin fadin kasar. A farkon watan Agusta, wasu sojojin Nijar 850 sun isa arewacin kasar Mali domin maye gurbin rukunin sojojin kasar na farko a cikin tawagar tabbatar da zaman lafiya ta MDD (MINUSMA).
Kasar Nijar dai na raba iyaka da kasar Mali bisa tsawon kilomita 400, baya ga haka al'ummomin kasashen biyu na magana harsunan Tamajek, Songhoi da Fulatanci da sauransu. (Maman Ada)