An kaddamar da kamfen bunkasa ayyukan baje koli karo na biyu na kungiyar tattalin arziki da kudin yammacin Afrika (UEMOA) a ranar Talata a birnin Yamai na kasar Nijar a karkashin jagorancin ministan kasuwacin kasar Alma Oumarou a yayin wani gagarumin biki.
Baje kolin na kungiyar UEMOA zai gudana daga ranar 13 zuwa 22 ga watan Disamba mai zuwa, kuma shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou zai jagoranci bikin bude shi wanda zai hada manyan 'yan kasuwa da masana'antu na wannan kungiya, haka kuma wata babbar dama ce ta yin musanya cikin hadin gwiwa domin cimma muradun kasashen Afrika da na kasa da kasa bisa hanyar bunkasa kasuwanci da musanya.
Kimanin rumfuna 250 za'a haka a dandalin taruruka na 'Palais des Congres' a birnin Yamai, domin gabatar da kayayyaki da fasahohi a yayin wannan baje koli.
Birnin Bamako na kasar Mali, ya shirya bikin baje kolin kungiyar UEMOA karo na farko a cikin watan Disamban shekarar 2008. (Maman Ada)