in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin wasannin SUKABE karo na 10 a Dosso na Nijar
2013-09-02 10:22:01 cri

Ministan al'adun kasar Nijar Ousmane Abdou ya kaddamar a ranar Lahadi a gidan samari da 'yan mata na Salma danrani dake birnin Dosso da bikin wasannin dunkulewar kasashen Afrika na SUKABE karo na 10 da aka aza a karkashin jagorancin uwargidan shugaban kasar Nijar madam Malika Issoufou kuma tauraruwar wannan biki. Fiye da 'yan wasan fasaha 220 da suka fito daga jihohi takwas na kasar Nijar da kasashe kusan goma na shiyyar kungiyar ECOWAS suke halartar wasannin wannan karo. An yi bikin wasannin tare da wani babban faretin tawagogin dake halarta wadannan wasanni karo na 10. Haka kuma an samu tawagogi da suka fito daga tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin uwargidan gwamnan jihar Kebbi dake makwabtaka da birnin Dosso, madam Assamaou Saidou Dangari, shugaban kwamitin tattalin arziki, al'umma da al'adu na kasar Nijar, Moussa Moumouni Djarmakoye da kuma mambobin gwamnati da 'yan majalisa. Wasannin gargajiyar sun soma gadan gadan tun ranar Lahadi da yamma, inda a tsawon mako guda, 'yan wasan da suka fito daga yawancin kasashen shiyyar za su fafata ta fuskar wasannin al'adu da na gargajiya. Bikin wasannin SUKABE, a cewar manajansa, Soumana Tini Wonkoye, wani dandali ne na matasa dake da manufar karfafa hadewar nahiyar Afrika da kuma jin dadin matasan Afrika, sannan wata dama ce ta ganin al'adun gargajiya da 'yan wasan fasaha na al'ummomin kasashe daban daban, musammun ma na shiyyar ECOWAS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China