Bukukuwan wannan karo na shekarar 2013 na babbar haduwar shekara shekara ta makiyayan kasar Nijar, da ma na kasashen dake makwabtaka da Nijar, da aka fi sani da sallar gishiri, ko "cure salee" da Faransanci sun soma a ranar Lahadi a garin Ingall mai tazarar kilomita 130 a yammacin jihar Agadez dake arewacin kasar ta Nijar a karkashin jagorancin faraministan kasar, malam Brigi Rafini, a gaban manyan mutane da baki da ke halartar wannan haduwa ta makiyaya.
Sallar gishiri ta kasance wani babban bikin shekaka shekara mafi muhimmanci a kasar Nijar a karshen damana, inda makiyaya Fulani da Abzinawa suke kawo dabbobinsu a yankin Ingall domin su yi kiwo, ganin yadda wuri yake da ciyayi dake kunshe da gishiri mai gina jikin dabbobi. (Maman Ada)