in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gina asibitin zamani a birnin Yamai na Nijar
2013-09-11 14:34:22 cri

Bisa tushen bunkasa huldar hadin gwiwa tare da Nijar ne, kasar Sin tana dauki niyyar gina wata babbar asibitin zamani a birnin Yamai mai iyar daukar fiye da gadaje 500, in ji jakadan kasar Sin a Nijar mista Shi Hu, bayan wata ganawarsa da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou a ranar Talata a birnin Yamai.

Za'a kaddamar da ayyukan gina wannan asibiti na jimillar kudin sefa fiye da biliyan 13 a cikin wannan wata na Satumba, in ji mista Hu.

A cewar hukumomin kasar Nijar, asibitin zai kasance na zamani kuma mafi girma daga cikin asibitocin kasar.

Haka kuma jakadan kasar Sin ya shaida wa manema labarai cewa, sun tattauna tare da shugaba Issoufou kan wani shirin gina layoyin isar da wutar lantarki bisa tsawon daruruwan kilomita daga Soraz zuwa Zinder, Maradi da Malbaza inda masana'antar siminti ta kasar take, gina wani kamfanin siminti da kuma shirin karfafa karfin samar da ruwan sha masu tsabta a birnin Damagaram.

A halin yanzu dai dangantaka tsakanin kasashen biyu ta shafi fannoni da dama wadanda suka hada siyasa, tattalin arziki, makamashi, al'adu, tsaro da kuma gine-gine, haka kuma wannan dangantaka ta kara fadada tare da shigar kamfanonin kasar Sin fannin harka da tace man fetur din kasar Nijar da hakar sinadirin uranium, musamman ma na yankin Azelik tare da kamfanin SOMINA a arewacin kasar. Tare da taimakon kasar Sin ne, Nijar ta shiga cikin jerin kasashe masu fitar da man fetur a duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China