in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban MISMA ya gabatar da ta'aziyarsa kan mutuwar wani janar din Nijar
2013-05-13 11:22:04 cri

Babban wakilin kungiyar AU na kasar Mali da shugaban tawagar rundunar sojojin kasa da kasa domin tallafawa kasar Mali na MISMA, Pierre Buyoya ya gabatar da ta'aziyarsa a ranar Lahadi bayan mutuwar birgediya janar Yaye Garba, mataimakin shugaban tawagar MISMA.

Sanarwar na mai cewa, mista Buyoya ya samu cikin kaduwa da bacin rai kan mutuwar birgediya janar Yaye Garba mai shekaru 55 da haifuwa. Haka babban jami'in ya aika ta'aziyarsa zuwa ga kungiyar AU, kungiyar ECOWAS da nahiyar Afrika baki daya, ga iyalin marigayin, har zuwa ga gwamnatin Nijar da al'ummar kasar baki daya, a cewar wannan sanarwa.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China