Jami'an kasashen Amurka, Rasha, Burtaniya, Faransa, da kasar Sin sun yi shawarwari na tsawon kusan sa'a daya a wannan rana a birnin New York, inda suka tattauna kan wani shirin kuduri da kasashen Amurka, Burtaniya, da Faransa suka tsara dangane da batun makamai masu guba na Syria. Shirin kudurin da ya bukaci Syria ta lalata makamanta masu guba bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka da Rasha. Daga baya, zaunannun kasashen nan guda 5 na kwamitin sulhu za su kara tattaunawa kan shirin a ranar Laraba 18 ga wata.
A nasa bangaren, babban sakataren MDD, Ban Ki-Moon cewa ya yi, kamata ya yi kwamitin sulhu ya hada kai sosai, tare kuma da hanzarta daukar matakai don yin yunkurin lalata makamai masu guba na Syria.
Bugu da kari, Ban Ki-Moon ya ce, a hakika mambobin kwamitin sulhu sun amince da yarjejeniyar da kasashen Amurka da Rasha suka cimma.Kuma kamata ya yi kwamitin ya dauki matakan da suka dace ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma kara da cewa, dole ne a ba da tabbaci wajen hana amfani da makamai masu guba, da duk wani irin makaman kare dangi yayin yake-yake. (Bilkisu)