Game da lamarin, zaunannen wakilin kasar Rasha da ke MDD Vitaly Churkin ya bayyana cewa, bai kamata a tabbatar da cewa, gwamnatin kasar Syria ce ta yi amfani da makamai masu guba bisa rahoton da aka bayar ba. Ya kamata a mai da hankali tare da yin nazari kan rahoton yadda ya kamata.
Zaunanniyar wakiliyar kasar Amurka da ke MDD Samantha Power ta nuna cewa, bisa bayanin da rahoton ya nuna, ana iya tabbatar da cewa, sojojin gwamnatin kasar Syria ne suke da karfin kai farmaki da makamai masu guba da dama kamar yadda shaidun suka nuna, kuma zaunannen wakilin Burtaniya dake MDD ya amince da ra'ayinta.
Ran 16 ga wata, firaministan kasar Syria Wael Nader al-Halqi ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Syria na da makaman da suka fi makamai masu guba wajen yaki da akokan gaba, idan za a iya daukar matakan soja tare da kaucewa asarar dukiyoyi da rayukan jama'a, gwamnatin Syria ba da ta nufin ganin kasancewar makamai masu guba. (Maryam)