130916-al-da-gwamnatin-syria-na-maraba-da-yarjejeniyar-da-kasashen-amurka-da-rasha-suka-cimma-game-da-makamai-masu-guba-na-syria-bilkisu
|
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov sun cimma wata yarjejeniya game da batun lalata makamai masu guba na kasar Syria a ranar 14 ga wata a Geneva. Daga baya kuma, kungiyar kasashen Larabawa wato AL da gwamnatin Syria sun yi lale marhabin da yarjejeniyar a ranar 15 ga wata. A nasu bangaren, 'yan adawa na Syria sun bukaci a yanke hukunci kan wadanda suka yi amfani da makamai masu guba, kana da hana sojojin gwamnatin kasar kara kai hari kan biranen kasar ta jiragen sama na soja.
Ministan watsa labaru na kasar Syria Omran Zoabi ya yi bayyani a ranar 15 ga wata cewa, Syria za ta bi yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen Rasha da Amurka game da makamanta masu guba. Yana mai cewa, bayan kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurorin da batun ya shafa, to Syria za ta aiwatar da yarjejeniyar. A yanzu haka ma ta soma shirya wata takarda game da wuraren da makamanta masu guba suke. Bugu da kari ya ce, kasar Syria za ta samar da sharuda masu sauki ga masu aikin binciken makamai na MDD yayin da suke gudanar da ayyukansu a kasar.
A yayin da yake zantawa da manema labaru na kasar Rasha a ranar 15 ga wata, ministan kula da harkokin sulhunta al'umma na kasar Syria, Ali Haider ya ce, gwamnatin Syria tana maraba da yarjejeniyar da kasashen Amurka da Rasha suka cimma kan yadda za a lalata makamai masu guba na Syria. Haider ya kara da cewa, yarjejeniyar za ta taimakawa jama'ar kasar wajen fita daga hargitsin da suke fuskanta, a waje guda, yarjejeniyar ta kawar da sharadin da wasu kasashe ke dogara akai na tayar da yaki, hakan zai hana kai harin da za a kai wa kasar ta Syria. A ganin Haider, yarjejeniyar ta kasance babbar nasara ga shugabannin kasar Rasha a harkokinsu na diplomasiyya, kana kuma nasara ce ga kasar Syria, saboda haka kasar ta yi godiya ga aminiyarta Rasha.
A wannan rana kuma, babban sakataren AL, Nabil Elaraby ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi maraba sosai da shirin yarjejeniyar da kasashen Amurka da Rasha suka cimma, a cewarsa wannan muhimmin mataki ne da aka dauka wajen warware matsalar Syria a siyasance, kuma zai samar da sharadi mai kyau don kiran taron Geneva karo na biyu kan batun Syria. A sa'i daya, ya yi kira ga bangarori daban daban da batun ya shafa da su taka rawar da ta kamata bisa tsarin MDD, da nufin tabbatar da tsagaita bude wuta a duk fadin kasar Syria, ta yadda za a samar da muhalli mai kyau ga jama'ar kasar wajen samun tallafin jin kai da na ba da jinya da suka wajaba.
A nasu bangaren kuma, 'yan adawa na kasar Syria a ranar 15 ga wata sun bukaci kasashen duniya da su hana gwamnatin Syria kai farmaki kan biranen kasar daga sama bisa tushen hana amfani da makamai masu guba, kana da yanke hukunci kan masu amfani da makamai masu guba.
Dakarun dake adawa da gwamnatin kasar Syria NCSROD sun bayar da wata sanarwa a wannan rana cewa, Rasha ta gabatar da wannan shawara game da mika makamai masu guba da gwamnatin Syria za ta yi da nufin gudun daukar matakin soja kan kasar, gwamnatin Assad ta amince da shawarar ce saboda tsoron daukar matakin soja. A ganin kungiyar NCSROD, gwamnatin Syria ta amfana daga wannan yarjejeniya a tsakanin Amuka da Rasha, tana mai cewa, gwamnatin Syria a yanzu haka tana daukar matakin soja ba kakkautawa a wurare daban daban na kasar, har ma ta kai farmaki daga sama kan wasu unguwowi, da kuma karin hare-haren da makamai masu linzami. Saboda haka, dole ne a hana gwamnatin Syria amfani da jiragen saman soja da manyan makamai wajen kai farmaki kan birane.
Wannan yarjejeniyar da kasashen Amurka da Rasha suka cimma ta gamu da adawa daga Salim Idriss, wato shugaban kungiyar adawa ta Syria wato Free Syrian Army. A yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 14 ga wata a birnin Istambul na kasar Turkiya ya bayyana cewa, kungiyarsa ba ta da nufin aiwatar da ko wane sashe daga yarjejeniyar, za ta kuma ci gaba da yaki har zuwa lokacin tumbuke mulkin Bashar.
Manazarta suna ganin cewa, ko da yake yarjejeniyar da kasashen Amurka da Rasha suka cimma game da batun makamai masu guba na Syria za ta taimaka wajen warware matsalar Syria ta hanyar siyasa, amma matsalar makamai masu guba na daya daga cikin hargitsin kasar Syria kawai, har yanzu ba a warware muhimman matsalolin da suka haifar da rikici a kasar ba, saboda haka, wace irin hanya ce da za a bi don canja yanayin da kasar ke ciki a siyasance, har yanzu ita ce babbar matsalar da ke gaban kasashen duniya. (Bilkisu)