in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba za ta amince ko wane bangare ya yi amfani da makamai masu guba ba, in ji wakilin kasar.
2013-09-17 15:30:22 cri
Ran 16 ga wata, zaunannen wakilin Sin da ke MDD Liu Jieyi ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta amince kowane ne ya yi amfani da makamai masu guba ba. Ya kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su bunkasa matakin warware batun Syria ta hanyar siyasa.

Mr. Liu ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta amince da yin amfani da makamai masu guba ba, kuma tana suka mai tsanani ga duk wadanda suka gudanar hakan. Bugu da kari, Liu ya ce kasar Sin na goyon bayan ayyukan bincike da MDD ke jagoranta, tare da dukufa wajen yin nazari kan rahotannin da aka gabatar.

Mr. Liu ya kara da cewa, a baya bayan nan, kasashen Rasha da Amurka sun kulla wata yarjejeniya kan batun zargin amfani da makamai masu guba na kasar Syria, matakin da kasar Sin ta yi maraba da shi sosai. Har ila yau, kasar Sin tana fatan gwamnatin kasar Syria za ta shiga yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba.

Mr. Liu ya jadadda cewa, hanya kadai da za a iya warware batun Syria ita ce ta siyasa. Ya ce kasar Sin tana burin ci gaba da yin cudanya da mu'amala tare da bangarori daban daban da wannan batu ya shafa don ba da taimako wajen warware matsalar kasar Syria ta hanyar siyasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China