A jiya Juma'a ne dai, kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky ya bayyana cewa, tawagar binciken ta riga ta kammala ayyukanta, ciki hadda bincikar zargin da ake yi cewa, an yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula a kasar ta Syria a ran 21 ga watan nan.
(Maryam)