Kungiyar "Syria-based National Coordination Body" ta bayar da sanarwa a ranar 2 ga wata cewa, tana adawa da kasar Amurka da aminanta dake yammacin duniya da su dauki matakan soja kan Syria. Sanarwar ta ce, harin da za a kai yana bisa tushen kiyaye moriyar Amurka da tsaron kasar Isra'ila ne, a maimakon kiyaye moriyar jama'ar Syria.
Kasashen duniya sun mayar da martani daban daban kan barazanar da Amurka ke yi wa Syria. Shugaban kwamitin kula da manufofin diplomasiyya na majalisar dokokin kasar Iran, Alaeddin Boroujerdi, wanda a yanzu haka ke yin ziyara a Lebanon ya nuna matsayin kasarsu kan batun, ciki har da tsaron kasar Syria, da kin yarda da daukar matakan soja kan Syria, da kuma yin Allah wadai da yin amfani da makamai masu guba. A nasa bangaren kuma, babban sakataren kungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen a ranar 2 ga wata yana mai cewa, kungiyar ba zata shiga batun daukar matakin soja kan Syria ba, amma kasashe mambobinta na iya tsaida kuduri da kansu game da batun.
A ranar 2 ga wata kuma, ofishin kakakin babban sakataren MDD ya sanar da cewa, a wannan rana tawagar binciken batun makamai masu guba ta MDD ta riga ta turo samfurin da abin ya shafa daga birnin Hague na kasar Holland zuwa dakunan gwaje-gwaje da aka tanada,, inda aka soma ayyukan nazari game da zargin da aka yi wa gwamnatin Syria na yin amfani da makamai masu guba. (Bilkisu)