in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori biyu masu arangama da juna a kasar Syria sun zargi juna kan yin amfani da makamai masu guba
2013-03-20 16:28:14 cri
Gidan telebijin na kasar Syria ya bayar da wani labari a ranar 19 ga wata cewa, dakaru masu adawa na kasar sun harba wani makami mai guba a yankin Aleppo a wannan rana, wanda ya haddasa mutuwar mutane 25 tare da raunatar mutane da dama. Amma hafsan hafsoshin dakarun dake adawa ya musunta wannan labari, saidai ya zargi sojojin gwamnatin kasar Syria da harbar makamai masu guba a wannan rana.

Game da wannan lamari, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru a ranar 20 ga wata cewa, yin amfani da makamai masu guba ya sabawa dokokin duniya. Kuma Sin tana kin amincewa da duk wani da ya yi amfani da irin wadannan makamai. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China