Kakakin Majalissar Martins Neserky yayi bayani ma manema labarai cewa bisa ga bayanan da majalissar tayi nazari akan su ya zuwa yanzu da kuma yarjejeniyar da majalissar ta cimma da gwamnatin kasar ta Syria,tawagar zata tashi zuwa kasar nan bada jimawa ba domin ta binciki wannan zargi na aikata wannan laifi a wurare uku da suka hada da Khan al-Asal.
Babbar wakiliyar majalissar a ofishin kula da sha'anin kwace damara Angela Kane, tsohon jami'in majalissar mai aikin binciken makamai a kasar Iraqi kuma shugaban tawagar binciken amfani da makamai masu guba a kasar Syria Ake Sellstrom sun ziyarci Damascus, babban birnin kasar a makon da ya gabata, kuma sun samu sakamako mai kyau na tattaunawar da suka yi da jami'an kasar kan yadda gwamnatin ta amince ta bada hadin kai ga tawagar majalissar a lokacin binciken da za su yi a kasar. (Fatimah)