A nasa bangaren, shugaba Bashar al-Assad na kasar Syria yi bayani a ranar 1 ga wata cewa, barazanar da kasar Amurka ke yi ba za ta hana kasar bin manufarta ba, Syria tana iya magance duk wani irin hari daga ketare.
A wannan rana kuma, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Syria, Faysal Mekdad ya ce, jawabin da shugaba Obama ya yi ya nuna cewa, yana dari-darin kai hari kan Syria. Ko shugaban kasar Amurka ko kuma shugabannin sauran kasashe, dukkansu ba za su iya bayar da hujja game da dalilan kaiwa Syria hari ba.
Bayan haka kuma, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya buga waya ga Ake Sellstrom, shugaban tawagar binciken batun makamai masu guba na Syria, inda ya bukaci da su hanzarta kammala nazarin bayanai game da zargin yin amfani da makamai masu guba a ranar 21 ga watan Agusta a karkarar Damascus.
Haka zalika, hukumar manyan kwamishinonin kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD ya bayar da rahoto a ranar 1 ga wata a Beirut cewa, ya zuwa yanzu yawan jama'ar kasar Syria dake neman matsayin 'yan gudun hijira a Lebanon ya kai dubu 716, wato ya karu da dubu 13 bisa na makon jiya. Yanzu suna samun tallafi daga wajen gwamnatin Lebanon da hukumomin duniya, ciki har da MDD. (Bilkisu)