Mataimakin shugaban kwamitin musulmi na kasar Sin kuma shugaban tawagar mahajattan shekarar bana na kasar Sin tare da ma'aikatansa, da suka isa kasar Saudiyya da jimawa, suka je tarbon wadannan mahajatta daga lardin Yunan.
Yang Zhibo ya ce, yawan maniyyatan shekarar bana na kasar Sin ya zarce 11800, kuma za'a jigilarsu a cikin jiragen sama na musamman 38 daga biranen Urumqi, Lanzhou, Yinchuan, da Kunming da Beijing, sannan kuma, za su sauka a binin Madina. Bayan da suka dan tsaya a wurin, maniyyata aikin hajji na kasar Sin za su hau motocin bus-bus don kai ziyara a birni mai tsarki wato Mekka, don jiran aikin hajji da Za' a fara aikin hajji daga bakin ranar 12 ga watan Oktoba bisa tsawon kwanaki 5 .(Bako)