in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahajjatan kasar Sin sun dawo gida bayan yin haji a Saudiyya
2011-12-04 17:20:13 cri
Ranar Lahadi 4 ga wata, jirgin sama na karshe mai dauke da musulman kasar Sin da suka kammala aikin haji a kasar Saudiyya ya sauka Beijing daga birnin Jidda na Saudiyya Arabiya. Ta haka dukkan musulman kasar Sin da suka je Saudiyya yin aikin haji sun dawo gida cikin koshin lafiya.

A wannan rana musulmai 324 da ke cikin wannan jirgin sama sun fito ne daga lardunan Jiangxi, Heilongjiang da Jilin da birnin Tianjin.

A shekarar da muke ciki, musulmai fiye da 13,700 na kasar Sin sun je Saudiyya yin haji. Hukumomin kasar Sin da abin ya shafa sun taimaka wa juna sosai, a kokarin tabbatar da ganin wadannan musulmai sun kammala yin haji yadda ya kamata. Kuma ayyukan jami'an sun samu gamsar da mahajjatan, da kuma bangaren Saudiyya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China