Mataimakin babban sakataren kungiyar kula da harkokin addinin musulunci na kasar Sin Jin Rubin ya bayyana cewa, a shekarar da ake ciki, gaba daya musulmai dubu 13 da dari 8 na kasar Sin za su tafi Makka domin aikin haji, wannan jirgin saman da ya tashi daga Lanzhou jiya shi ne na farko da aka yi hayarsa a Sin, daga bisani kuma akwai sauran jiragen guda 40 da za su tashi zuwa Makka daga Beijing, Yinchuan, Urumqi, Kunming da dai sauran birane daya bayan daya.
Gwamnatin kasar Sin ta samar da hidima mai inganci ga manityyata aikin haji a fannoni daban daban, ciki har da masu ba da jagoranci, masu kula da harkokin addini, likitoci da kuma masu dafa abinci. (Maryam)