in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maniyyata aikin Hajji daga kasar Sin na cigaba da tashi zuwa kasa mai tsarki
2012-10-08 15:50:04 cri

Kawo yanzu, kimanin karin maniyyata aikin Hajji 332 ne daga yankin Ningxia dake arewa maso yammacin kasar Sin suka tashi zuwa birnin Macca, domin gudanar da aikin Hajji daga kasar a bana. Maniyyatan da suka tashi a yammacin ranar Lahadi, na cikin jerin musulmai 13,800 da ake tsammanin za su halarci aikin Hajjin na bana daga kasar Sin, a cewar mataimakin hukumar lura da harkokin musulmin yankin Li Yushan.

Tuni dai kimanin maniyyata 2,700 suka isa birnin Macca daga yankunan dake lardin Gansu, a jigila 8 da ta gabata, cikin wani tsarin jigilar maniyyatan da aka tanadawa jirage 41 domin tabbatar da nasararsa.

Daga yankin Ningxia dake da yawan musulmi, ana sa ran maniyyata 2676 ne za su halarci aikin Hajjin na bana.

Ita dai kasar Sin na da adadin mabiyan addinin musulunci kimanin miliyan 20, wadanda kusan rabinsu 'yan asalin kabilar Hui ne, hakan nan baya ga musulmai mazauna yankin Ningxia, yawa-yawan al'ummar musulmin kasar ta Sin na zaune ne a lardunan yammacin kasar, da suka hada da lardunan Qinghai, da Gansu, da kuma Yunnan, baya ga wadanda ke lardin Xinjiang mai cin gashin kansa na kabilar Uygur.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China