A ran 28 ga wata da karfe 9 da minti 40 na safe, rukunin farko na mahajjatan jihar Ningxia sun cimma nasarar kammala aikin hajji, kuma sun koma gida lami lafiya daga birnin Makka.
Mutane 332 jirgin sama na farko iso kasar Sin, kuma mahajjatan karshe na jihar Ningxia za su koma birnin Yinchuan a ran 3 ga watan Disamba.
Bayan awoyi 11 cikin jirgin sama, tare da gajiya amma wannan bai hana alhazan nuna farin cikinsu ba, tare da bayyana wa iyalansu ayyukan ibadar da suka yi a birnin Makka.
Bisa labarin aka bayar an ce, musulmai 2656 na jihar Ningxia suka gudanar da aikin hajji a wannan shekarar a kasar Saudi Arabiya, kuma yawansu ya kai kashi 19.2 cikin dari na dukkan mutanen kasar Sin da suka yi aiki hajji a kasa mai tsarki.(Lami)