in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hare-hare ga tawagar masu bincike na M.D.D.
2013-08-27 14:41:49 cri

A ranar 26 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Sham ya bayar da labarin cewa, a wannan rana, yayin da tawagar masu bincike kan makamai masu guba ta M.D.D. ta shiga yankin Al-Muadamieh da ke wajen birnin Damascus, wasu dakaru masu dauke da makamai sun kai wa tawagar hari, a kan hanyar, ma'aikatan tsaron kasar ta sham na raka tawagar zuwa yankunan dake karkashin ikon gwamnati. Game da wannan lamari, gwamnatin Sham ta zargi 'yan ta'adda da aika hakan.

A ranar 26 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Sham ya ruwaito bayanin jaridar Izvestie ta kasar Rasha, game da tattaunawar da ta yi da shugaban kasar Sham Bashar Al-Assad, inda Shugaba Assad ya jaddada cewa, duk zargin da aka yi wa sojojin gwamnatinsa, na amfani da makamai masu guba ba gaskiya ba ne. Ya sake nanata cewa, ba wai juyin-juya hali ne ke wakana a kasar Sham ba, kawai dai ta'addanci ne da aka aiwatarwa da nufin sauya gwamnatin kasar, kuma Sham ba za ta zama 'yar amshin shatar kasashen yammacin duniya ba.

A dai wannan rana, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya yi kashedin cewa, duk wani matakin soji da za a dauka kan Sham, idan ba a samu amincewar kwamitin sulhu na M.D.D. ba, zai keta dokokin kasa da kasa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China