in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Siriya ta amince da masu bincike na M.D.D.
2013-08-26 16:46:08 cri
A ranar 25 ga wata, ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Siriya ta ce, kwanan baya, gwamnatin Siriya ta riga ta cimma matsaya guda da wakilin koli mai kula da harkokin kwance damara na M.D.D. Angela Kane da ya kai ziyara a kasar kwanan baya, inda ta amince da rukunin masu binciken makamai masu guba na M.D.D. da ya je yankin karkara na birnin Damascus don gudanar da bincike game da jita-jitar da aka bayar na wai yin amfani da makamai masu guba a wurin.

A ranar 25 ga wata, sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta kakakinsa, inda ya bayyana cewa, bayan da aka samu matsaya guda da gwamnatin Siriya game da hanyoyin yin hadin gwiwa, a ranar 26 ga wata, rukunin masu binciken makamai masu guba na M.D.D. zai gudanar da bincike a wurin da ake zargi take amfani da makamai masu guba.

A ranar 25 ga wata, fadar White House ta Amurka ta ba da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, a wannan rana, shugaban kasar Amurka Barack Obama da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande suka yi waya, inda shugabannin kasashen biyu suka dora muhimmanci sosai game da jita-jitan da aka samu cewa gwamnatin Siriya ta yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula a yankin karkara na birnin Damascus, kuma sun amince da cewa, za su ci gaba da tattaunawa game da batun.

Ban da wannan kuma, a ranar 25 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Alexander Lukashevich ya bayyana cewa, gwamnatin Siriya ta amince da rukunin masu bincike na M.D.D. da ya je binciken makamai masu guba, wannan ya bayyana sakamakon kokarin da gwamanatin Rasha da ta Siriya suka yi, kuma idan aka zargi gwamnatin Siriya da ta yi amfani da makamai masu guba kafin an samu sakamakon bincike, za a samu babban kuskure.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China