Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya gana da tawagar 'yan adawar kasar Syria
Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Jumma'a 13 ga wata cewa, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Zhai Jun ya gana da tawagar 'yan adawar kasar Syria a jiya Alhamis 12 ga wata a nan birnin Beijing, inda Zhai Jun ya jaddada cewa, hanyar siyasa ita ce hanya daya kawai wajen warware batun Syria, yana fatan tawagar 'yan adawar kasar Syria za su yi amfani da damar da suke da ita don samar da hanyar tattaunawa da gwamnatin kasar Syria da kungiyoyin adawar kasar don samar da sharadi wajen kaddamar da shawarwarin siyasa a kasar.
Game da halin da ake ciki a kasar Syria yanzu, Hong Lei ya jaddada cewa, tabbatar da zaman lafiya da na karko a kasar Syria shi ne abin da ya dace da moriyar kasa da kasa. (Zainab)