in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon bai samu rahoton binciken makamai masu guba na kasar Syria ba
2013-09-14 17:39:02 cri
A ranar 13 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya halarci taron dandalin tattaunawa kan batun mata na kasa da kasa da aka yi a hedkwatar MDD dake birnin New York. Yayin da yake tsokaci kan batun Syria, Mr. Ban ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su dakatar da ta da jijiyar wuya, su kuma fara gudanar da shawarwari a tsakaninsu. Sai dai abin da ya fi jan hankulan dukkan kafofin watsa labarai shi ne, Mr. Ban Ki-moon ya bayyana cewa, rahoton bincike da MDD ta yi, zai tabbatar da amfani da makamai masu guba a kasar Syria. Hake ne, ya sa aka ganin cewa, tuni Mr. Ban Ki-moon ya nazarci rahoton binciken makamai masu gubar kasa ta Syria. Sai dai yayin taron manema labaran da aka yi a wannan rana, kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ya musanta wannan hasashe, yana mai cewa ba a sanya lokacin da za a fidda rahoton ba.

Mr. Farhan Haq ya bayyana cewa, ba wanda zai iya bayyana abin da ke cikin rahoton a yanzu haka ba.

Har ila yau, bisa labarin da aka samu, an ce, mai kula da harkokin tawagar bincike Ake Sellsteom zai tashe zuwa birnin New York a karshen makon nan da muke ciki, don gabatar wa Ban Ki-moon rahoton da aka dade ana dakonsa. Bugu da kari, an ce, Mr. Ban Ki-moon ya yi alkawari mika wa mambobin kwamitin sulhu na MDD wannan rahoto, da zarar ya karbe shi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China