Rahotanni dai na bayyana cewa, yayin zaman sirri da mambobin majalissarta su 155 suka yi a jiya Jumma'a, an bayyana sunan Ahmad Tumeh al-Khader, a matsayin dan takarar mukamin mafi dacewa. Baya ga batun zaben Firamanistan rikon kwarya, ana sa ran SNC za ta bayyana matsayarta don gane da shawarar da shugaban kasar Rasha ya gabatar game da kasar Siriya.
Yayin wani taron 'yan jarida da ya gudanar, jagoran sashen yada labaran kungiyar ta SNC Khalid Saleh, ya bayyana cewa gamayyar kungiyar ta 'yan adawa na da matukar burin ganin kasashen duniya sun amince da shawarar hukunta wadanda ke da hannu, cikin hare-hare da makamai masu guba da aka kai kan fafaren hula a kasar ta Siriya. Har ila yau Saleh, ya jaddada bukatar samun karin kudaden tallafi ga 'yan adawar daga kasahen ketare. (Saminu Alhassan)