Shugaba Xi ya nuna yabo ga kokakin da sabuwar gwamnatin kasar Iran ta yi wajen warware matsalar nukiliyar kasar, kuma yana fatan za a ci gaba da yin shawarwari tsakanin bangarorin daban daban da abin ya shafa don cimma nasarar warware matsalar. Mista Xi ya kuma kara da cewa, kasar Sin za ta dukufa wajen ba da taimako don a warware matsalar ta hanyar yin shawarwari da kuma nuna girmamawa ga ikon kasar Iran.
Yayin ganawar, shugaba Rohani ya sake jaddada matsayin kasar Iran wajen yin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya, kuma za ta ci gaba da shirin nukiliyar kasar bisa dokokin kasa da kasa da kuma dokar hana yaduwar nukiliya ta kasa da kasa. Za ta yi hadin gwiwa tare da hukumar makamashin nukiliyar kasa da kasa don kawar da damuwar da gamayyar kasa da kasa ke nuna wa shirin nukiliyar kasar. (Maryam)